Tsohon gwamnan jihar Enugu, Mista Sullivan Chime a ranar Talata ya yi watsi da rade-radin cewa ya karbi kudi daga hannun Mista Peter Mbah na jam’iyyar PDP domin ya amince da shi a matsayin gwamna na gaba.
Da yake mayar da martani game da zargin da aka yi, Chime ya ce ya amince da Mbah, Shugaban Kamfanin Pinnacle Oil saboda irin hazakarsa da kwarewar sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwankwaso Bai Taya Tinubu Murna Ba,Kan Zaben Da Yake Cike Da Kura-kurai – NNPP
Tsohon gwamnan jihar kuma jigo a jam’iyyar APC a jihar Enugu ya ce yana goyon bayan Mbah domin cigaban jihar.
Ya jaddada cewa dan takarar gwamna na PDP zai kara wa jihar kima.
“Mutane sun ce na karbi kudi domin amincewa da dan takarar gwamna na PDP, amma ba gaskiya ba ne.
“Na yi nazarin sahihancin dukkan ‘yan takarar kuma na gamsu cewa Mbah zai taka rawar gani fiye da sauran.
“A watan Maris, zan cika shekara 64 kuma ina son kyakkyawar makoma ga jikoki na. Tare da Mbah, an tabbatar da makomar jihar Enugu kuma ta tabbata,” in ji shi.
Chime ya kara da cewa ya kamata mutane su zabi cancanta, halayya da iya aiki ba jam’iyya ba, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta mulki jihar Enugu ba.
Ya bayyana Mbah a matsayin wanda ya san abin da zai yi a kowane lokaci kuma ana iya tunkararsa don neman shawara da gyara.
“Da abin da ya yi a Pinnacle Oil and Gas, zai canza jihar kuma ina kira ga mutane da su fito ranar 11 ga watan Maris su zabi Mbah,” in ji Chime.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar Enugu da su guji tashin hankali a lokacin zabe, su kuma yi zabe cikin hikima.
Chime ya ce ya bar PDP ya koma APC ne saboda Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi da ke zaune ba ya yin wani abin da ya kamata ba.
“Na bar PDP zuwa APC ne saboda na gano cewa abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata,” inji shi.
Chime ya kuma musanta cewa ya koma jam’iyyar APC ne domin kaucewa kamawa da binciken harkokin mulki a matsayin gwamnan jihar Enugu. (NAN)
A wani labarin kuma, FG Ta Daga Likafar FMC Lokoja Zuwa Asibitin Koyarwa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sabunta Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi zuwa asibitin koyarwa.
Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Lokoja, Farfesa Akinwumi Olayemi, a ranar Talata, ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai na hadin gwiwa a harabar makarantar Adankolo da ke Lokoja.