Ban taɓa yin nadamar shiga aikin Ɗan Sanda ba — CP Mai barin gado na Kano
Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Kano mai barin gado, Sama’ila Dikko, ya ce bai taɓa nadamar shiga aikin ƴan sandan Najeriya ba a shekaru 35 da ya yi yana aiki.
CP Sama’ila Dikko ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga jami’an Rundunar Ƴan Sandan jihar Kano na bankwana a hedikwatar ƴan Sanda da ke Bompai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kama barayin shanu 18, sun kwato dabbobi 772 a Gombe
CP wanda ya kai shekarun ritayar aiki ya shawarci jami’an ‘yan sanda da su riƙa bin ka’idojin aikin a koda yaushe, kuma su guji duk wani nau’i na cin hanci da rashawa.
CP mai barin gado ya yaba da irin goyon baya da haɗin kai da ya samu a lokacinsa daga manyan jami’an gudanarwa na rundunar ta Kano, da jami’ai wanda ya kai ga nasarar da aka samu ta fuskar tsaro a Kano.
CP Dikko ya buƙaci jami’ai da jami’an ‘yan sandan Najeriya da su kara ƙwazo da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
“Ina ba ku umarni da ku kasance cikin shiri a ko da yaushe, domin a ko da yaushe masu aikata laifuka suna bin ku, kuma za su ɗauke ku idan ba ku cikin shirin a kowane lokaci”
Ya yaba wa ƙoƙarin babban sufeton ƴan sanda na kasa akan ingantaccen tsarin tabbatar da inganta walwalar ƴan sanda.