Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, ya yi watsi da rahotannin kafafen yada labarai dake cewa yana fatan tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2027
Dan takarar shugaban kasar ya kuma musanta cewa yayi magana kan wadanda gwamnatin tarayya ta nada
Mista Obi, wanda kuma tsohon gwamnan Anambra ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Asabar a Legas
Dan takarar shugaban kasar ya bayyana duka rahotannin biyu a matsayin na bogi, inda ya yi nadama kan yadda siyasar Najeriya ta durkushe a matsayin da ake amfani da kafafen yada labarai a yanzu wurin yada labaran karya
Ya ce na lura da wani tsari da ya kunno kai, inda rahotannin kafafen yada labarai na bogi da labarai ke saka labaran karya a shafukansu
Abubuwa biyu na baya-bayan nan da suka shafi maganar da nake cewa ina fatan tsayawa takara a 2027 akan wata hira da ake zaton Arise TV tayi dani
Wannan bai taba faruwa ba, na biyu kuma game da yadda ake cewa wai ina saka ido akan wadanda shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nada mukamin ministoci shima wannan karya ce tsagwaronta
KARANTA NANAn Samu Wani Dake Kwaikwayon Maganar Bola Tinubu A Wajen Taro – BIDIYO
Dan takarar shugaban kasar ya ce ba zai bari labaran karya su karkatar da hankalinsa ga sabuwar Najeriya ba, wanda ya dage cewa mai yiyuwa ne
Mista Obi ya ce hankalinsa da na kungiyar ‘Obidient’ da yake jagoranta ba za su yi kasa a gwiwa ba daga ainihin manufar samar da sabuwar Najeriya, wanda suke ganin zai yiwu
Ya ce a gare shi, zai ci gaba da yin magana kan batutuwan da suka shafi kasa ta hanyar sanannun labarai da kayan aikin jarida amma tabbas ba zai damu da kansa da arha ba
Mista Obi ya kuma ce ba a taba mayar da hankalin mabiyansa kan nade-nade da mukamai na siyasa ba
A WANI LABARIN KUMAGwamna Buni ya jajantawa Sakataren Kungiyar ‘Yan Jaridun kan rasuwar matar sa
Ba’a taba ba da fifikon mu akan mukamai na siyasa ko girman kai ba face dora al’umma a kan turba mai kyau da zurfafa DIMOKURADIYYAR mu ta hanyar taimakawa wajen daukaka da karfafa wadanda aka zalunta a cikin al’ummarmu