Shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Nairobi na kasar Kenya, inda zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka don halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na 5 na kungiyar Tarayyar Afirka AU.
Punch ta rawaito cewa Tinubu Ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila da Dele Alake, mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa, da dabaru.
KARANTA WANNAN: Munafunci Ne Cafke Emefiele Ba Tare Da Buhari Ba — Lauyoyi
Tinubu zai halarci taron ne a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya da kuma sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS.
Taron mai taken “Haɓakar aiwatar da yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka” zai tattaro ofishin Majalisar AU, wanda ya ƙunshi shugabannin ƙasashe da gwamnatoci daga Comoros, Botswana, Burundi da kuma Senegal, tare da shugabanni daga ƙasashe takwas na tattalin arzikin yankin.
Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala taron.
A wani labarin kuma,Tallafi: Masana sun gargadi Tinubu kan raba dubu 8,000 ga talakawan Najeriya
Wani masani kan harkokin kudi, Gbenga Adeoye, ya roki shugaba Bola Tinubu da ya kyale kudirin gwamnatinsa na raba Naira 8,000 ga talakawan Najeriya miliyan 12 cikin watanni shida.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasar ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa data amince da raba Naira Biliyan 500, wanda ake kyautata zaton za a raba wa talakawan Najeriya a matsayin tallafin rage radadin da ake samu na cire tallafin man fetur.
A cikin wasikar, Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tura Naira 8,000 duk wata ga magidanta miliyan 12, masu karamin karfi wanda hakan zai ninka ya zuwa kusan mutane miliyan 60.