Jurgen Klopp ya ce ba zai bar Liverpool ba har sai an ce ya tafi, yana mai nuni da wani gagarumin garambawul ga ‘yan wasansa a karshen kakar wasa ta bana. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Rashin nasara a gasar Premier karo na shida a karshen mako na nufin zakarun na 2020 suna da yazarar maki 10 kasa da na hudun farko yayin da aka ruga aka fafata rabin kakar wasa ta bana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Najeriya Miliyan 25 Na Fuskantar Barazanar Yunwa — UNICEF
Klopp a bara ya rattaba hannu kan kwantiragin cigaba da zama a Liverpool har zuwa 2026 kuma kocin mai shekaru 55 ya jaddada sallamarsa ne kawai zai hana shi kaiwa wannan lokaci.
Klopp, wanda kungiyarsa za ta kara da Wolves a wasan zagaye na uku na gasar cin kofin FA ranar Talata, ya kuma yi watsi da shawarar cewa ‘yan wasan da suka dade suna aiki sun daina sauraronsa ko jin maganarsa a yayin da kuniyar take wasa.
A wani labari kuma, Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Batun Jefa Kuri’a Batare Da PVC Ba
Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 30 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan karar da aka shigar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC. Kamar yadda Chennels TV ta ruwaito.
Masu shigar da kara sun hada da– Barista Emmanuel Chukwuka da Bruno Okeahialam inda suke neman umarnin tilastawa INEC ko dai ta baiwa wadanda suka yi rajistar katin zabe na dindindin (PVCs), ko kuma su ba da damar yin amfani da katin zabe na wucin gadi ko kuma lambar tantance masu zabe (VIN) damar kada kuri’a a zaben shekarar 2023.