Ma’aikatan bangaren sharia a Jihar Edo sun bijire wa umarnin uwar kungiyar su ta shiga yajin aiki kan abin da suka kira darasi da suka koya a 2015.
Ma’aikatan da suka fita aiki a babbar Kotun Jiha dake birnin Benin da sauran ofisoshinshari’a sun bayyana cewa a shekara ta 20215 sun yi kuskuren shiga yajin aiki inda aka aiwatar da tsarin nan “Ba Aiki, Ba Albashi, don haka a wannan karon ba z a su yi wannan kuskuren ba.
Kungiyar Ma’aikatan Bangaen Shari’ar sun kira wannan yajin aiki ne da zummar gwamnati ta biya musu bukatar su ta yancin gashin kan su.
To sai dai ma’aikatan sun ce babu ruwan su da umarnin kungiyar domin a shekarar 2015 sun yi makamancin wannan yajin aiki, kuma ba a bniya su albashi ba kafatanin iya lokacin da suka shafe suna yajin aikin.
“A shekarar 2015 mun shiga yajin aiki haka, kuma gwamnati ta yi kirmimis ta ki biyan mu albashi a wanchan lokacin, kuma kungiyar ta janye jikin ta ba ta sa baki ba, kuma har kawo lokacin da nake wannan magana ba a biya mu albashin ba” Cewar wani ma’aikaci da ya bukaci a sakaye sunan shi.
Da yake zantawa da manema labarai shugaban Kungiyar a jihar Edo Uyi Ogieriakhi ya ce sun samu labarin a kurarren lokaci wanda haka n ne ya sa ba su samu damar wayar da kan mambobin nasu ba.