A yayin da ake cigaba da zaman ɗar-ɗar biyo bayan jawabin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yayi kan tsofaffin kuɗi, bankuna sun cigaba da karɓar tsofaffin kuɗi a Najeriya.
Bankunan kasuwanci a Najeriya, a safiyar yau Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, sun cigaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1,000 daga hannun kwastomomin su. Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Ƙarancin kuɗi: Matashi ya bayar da omo domin a bashi abinci
Hakan ya saɓawa sanarwar da babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar inda bankin ke cewa bai umurci bankuna da su karɓi takardun tsofaffin kuɗin naira na N500 da N1000 daga hannun kwastomin su ba.
Haka kuma karɓar tsofaffin takardun kuɗin da bankunan ke yi yaci karo da umurnin CBN na cewa duk mutanen da suke da tsofaffin kuɗin da ba su kai naira dubu ɗari biyar ba (N500,000), da su garzaya bankin su ajiye kuɗaɗen su.
Bankunan dake cigaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗi a hannun kwastomomin su sun haɗa da: GT Bank, First Bank, Fidelity Bank, da Sterling Bank.
Canjin Kudi: Idan har halastaccen kuɗi ne da kai, ka kai shi CBN – Bashir Ahmad ga Ganduje
Bashir Ahmad, mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwa na zamani, ya jajirce wajen ganin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kai tsofaffin takardun kudinsa na naira zuwa babban bankin Najeriya, CBN, idan har halastacce ne.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Ahmad yana mayar da martani ne ga Ganduje, wanda ya caccaki manufar sake fasalin Naira, ya kuma bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na durkusar da dimokuradiyya da kuma zagon kasa ga babban zabe mai zuwa.