Karamin ministan albarkatun man fetur, Dr Timipre Sylva, ya ce Najeriya, na asarar gangar danyen mai 400,000 a kullum ta hanyar satar shi daga bata gari.
Sylva ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da ya kai wa Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Owerri.
Ya bayyana wannan nakasu da cewa babban kalubale ne, da zai ci gaba da haifar da koma baya ga ci gaban kasarnan.
Ya kuma bayyana nadamar sa, kan yadda gazawar kasar nan, wajen samu tsaikon fitar da kason kungiyar OPEC, wanda ya kamata ace ana fitar a kullum, inda yanzu adadin yayi kasa, daga ganga miliyan 1.8 zuwa ganga miliyan 1.4, sakamakon satar danyen man.
Ministan ya yi gargadin cewa irin wannan babban asara na tattalin arziki na iya gurgunta tattalin arzikin kasar idan ba a yi la’akari da matsalar yadda ya kamata ba.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda wannan barazana ta ci gaba da wanzuwa, duk da kokarin da gwamnatin tarayya da na Jihohi ke yi wajen dakile ta.
Sylva ya ce ba za a iya magance matsalar satar danyen mai a Abuja kadai ba.
Don haka ministan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai don magance matsalar satar danyen man baki daya.