Mataimakin shugaban kulob ɗin FC Barcelona, Rafa Yuste, ya tabbatar da cewa kulob ɗin ya tuntuɓi Lionel Messi domin duba yiwuwar dawowar sa kulob ɗin.
Ɗan wasan na ƙasar Argentina ya bar Barcelona cikin ƙwalla a shekarar 2021. Daga nan ya koma Paris Saint Germain a kyauta inda ya sanya hannu akan kwantiragin shekara biyu wacce zata ƙare a ranar 30 ga watan Yunin 2023. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya Zasu Tabbatar Da Sharbar Romon Dimokaradiyya ƙarƙashin Tinubu – Emokpaire
Yarjejeniyar da Messi ya ƙulla da PSG akwai zaɓin ƙara shekara ɗaya, wacce har yanzu ɗan wasan bai gama yanke hukunci akai ba.
Da yake magana a ƙasar Spain yayin tattaunawa da ƴan jarida, Yustre, ya tabbatar da niyyar kulob ɗin na sake dawo da ɗan wasan.
“Leo Messi da iyalan sa sun san irin son da nake musu. Da ni aka tattauna amma ba a samu nasara ba wacce muke fata.” A cewar Yustre inda yake tuno yadda ɗan wasan ya bar kulob ɗin.
“Tabbas zan yi matuƙar son ya dawo nan saboda abinda hakan zai janyo mana ta ɓangaren wasa, jindaɗi da kuma tattalin arziƙi. Eh tabbas muna tattauna da su.”
PSG Na Duba Yiwuwar Raba Gari Da Lionel Messi
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa Paris Saint Germain na shirin rabuwa da Lionel Messi idan kwantiragin sa ta ƙare.
Paris Saint-Germain na shirin raba gari da Lionel Messi a ƙarshen kakar 2022/23 lokacin da kwantiragin sa da kulob ɗin zata ƙare.
Messi da PSG suna cikin tattaunawa kan sabunta kwantiragin sa, amma abubuwan da suke faruwa cikin ƴan kwanakin nan sun sanya kulob ɗin sun takawa tattaunawar birki inda suke sake duba matsayar da suke kanta a baya