Basaraken gargajiyar Yaba da ke yankin Abaji a babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Abdullahi Adamu ya rasu.
Wani dan gidan marigayin Shuaibu Abdullahi ya shaida wa Daily Trust cewa marigayi Etsu na masarautar Yaba ya rasu ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa sallar magriba, a cikin fadarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Ya Sa Ban Goyi Bayan Peter Obi Ba – Wike
Shu’aibu ya ce sarkin mai shekaru 62 ya fadi kwatsam sai mukarrabansa suka garzaya da shi zuwa babban asibitin Abaji inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Yace; “Nan da nan ya fado, suka shigar da shi cikin motar zuwa asibiti. Amma abin takaici da isarsu asibitin, likitoci sun tabbatar da rasuwarsa.”
An dauke gawar daga asibiti zuwa Yaba, inda aka yi jana’izarsa da karfe 9 na safiyar ranar Juma’a 10 ga watan Maris.
A wani labarin kuma, Ba Zamu Taba Yin Watsi Da Peter Obi Ba – Dan Takarar Gwamnan LP
Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party, LP, a jihar Taraba, Sen Joel Danlami Ikenya, ya karyata zargin cewa jam’iyyar reshen jihar ta yi watsi da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, zuwa wata jam’iyya.
Ikenya, wanda ke mayar da martani game da amincewar da ake zargin ya yiwa jam’iyyar PDP, dan takarar gwamna a jihar, Kefas Agbu, ya kuma musanta cewa ya bar takara inda yace “har yanzu ina cikin takara”.