Hukumar inshorar ajiya ta Najeriya NDIC ta gargadi abokan huldar bankuna da sauran jama’a da su guji nuna bayanan bankunan su inda ta ce masu damfara suna kara yin kirkire-kirkire.
Hukumar NDIC a cikin gidan yanar gizon ta ranar Juma’a ta ba da shawarwari hudu ga abokan cinikin banki don kiyaye asusunsu daga ‘yan damfara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Basaraken Gargajiya Ya Fadi,Ya Rasu A Fadarsa
Hukumar ta ce ya kamata kwastomomin su tabbatar da cewa wayoyinsu suna da matakan tsaro na kalmomin sirri kuma kada su bayyana kalmar sirri ta wayar hannu ko ta banki ga kowa.
NDIC ta kuma gargadi abokan huldar bankunan da su tabbatar da cewa an tsare tambarin su kuma sauran bangarorin ba su samu damar shiga ba.
Hukumar ta kuma bukaci kwastomominsu da su tabbatar da cewa lambobin katin cirar kudi da kuma Katin CVV ba a fallasa su ga mutane.(NAN)
A wani labarin kuma, Dalilin Da Ya Sa Ban Goyi Bayan Peter Obi Ba – Wike
Gwamna Nyesom Wike na Rivers ya ce bai goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi ba a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu saboda babu wanda ya tattauna da shi kan shugabancin Igbo.
Sakataren yada labarai na kungiyar Ohaneze Ndigbo na duniya, Dr Alex Ogbonnia ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Enugu cewa Wike ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar ta yi da shi a Fatakwal a ranar Alhamis.