Gabanin gudanar da zanga-zangar da kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC suka shirya yi a fadin kasar a ranar Laraba 2 ga watan Agusta, 2023, kan karin farashin man fetur, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Auwal Musa Muhammad, ya gana da shugabannin NLC da JPNC domin lalubo hanyoyin tabbatar da yin zanga-zangar cikin lumana.
Taron wanda ya gudana a hedikwatar ‘yan sandan jihar Bauchi da ke kan titin Yandoka a ranar Talata, ya samu halartar wakilan shugaban NLC na jihar Shu’aibu Dauda da shugaban JPNC na jihar Ibrahim Maikudi.
KARANTA WANNAN: Jerin Sunayen Ministoci: Tinubu Bai Yi Kuskure Ba – Yari
Kwamishinan na ‘yan sanda Auwal ya jaddada bukatar yin hadin gwiwa da shugabannin kungiyar domin samar da zaman lafiya da ya mamaye jihar da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa kafin muzaharar, lokacin da kuma bayan gudanar da zanga-zangar.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma jaddada aniyar sa na tabbatar da tsaron dukkan ‘yan kasa a duk tsawon wannan atisayen.
Ya kuma yi gargadin cewa duk wani yunkuri na bata-gari na amfani da lamarin domin tada kayar baya kamar barna, gungun ‘yan daba, da karbar kudi za a fuskanci turjiya sosai.
“Hukumar ba za ta lamunci duk wani aiki da zai kawo cikas ga zaman lafiya a jihar da kuma kasarmu mai daraja ba,” in ji Auwal.
A jawabansu daban-daban, shugabannin kungiyoyin sun amince da hada kai da rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi a fannin yada labarai domin gudanar da zanga-zangar lumana ta hanyar daukar matakan da suka dace.
Yace matakan sun hada da tantance dukkan wakilansu da za su halarci wannan muzaharar da sauran na cikin gida duba matakan da za su ba su damar gudanar da zanga-zangar cikin nasara.
A wani labarin kuma, Kano: Hukumar Kula Da Asibitoci Ta Kori CMDs 3, Ta Dakatar Da Likitoci
Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Dakta Mansur Nagoda, ya amince da korar manyan jami’an lafiya na wasu asibitoci uke dake a jihar.
Asibitocin da abin ya shafa sun hadar da Asibitin Imam Wali,Asibitin Abubakar Imam Urology Center da kuma asibitin haihuwa na Nuhu Bamalli tare da maye gurbinsu da wasu jami’an lafiya cikin gaggawa.