Kungiyar Kwadago ta Najeriya, a ranar Talata da daddare ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labarin yiwuwar dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar da aka shirya farawa ranar Laraba, Punch ta rawaito.
Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Joe Ajaero, ta ce za a gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka tsara a manyan biranen kasar.
KARANTA WANNAN: Bauchi: Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Gana da Shugabannin Kwadago, Ya Nemi Wata Bukata
Tun da farko a wata ganawa da manema labarai da shugaban kungiyar na kasa, babban sakataren kungiyar ta NLC, Emmanuel Ugboaja, ya bayyana cewa majalisar na iya sake duba matsayar ta a kan shirin yajin aikin.
Sai dai kuma,bayanin na Ugboaja ya haifar da cece-kuce tare da labarai game da yiwuwar dakatar da yin zanga-zangar a fadin kasar.
Sanarwar wacce aka wallafa a shafin Twitter na NLC ta ce, “Ku yi watsi da jita-jita ta karya, NLC ba ta rabu ba. Mu cibiya ce mai haɗin kai kuma mai ƙarfi. Za a gudanar da zanga-zangar ne a gobe Laraba a duk fadin kasar.”
Tun da farko, Ajaero, a tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana cewa NLC ba ta da dalilin dakatar da yajin aikin da ta ke shirin yi.
“Ba mu da wani dalili na soke zanga-zangar da aka shirya. Idan muka dakatar Zan iya gaya muku cewa taron ya yi yawa sosai,” in ji Ajaero.
Hakazalika, mataimakin shugaban kungiyar NLC, Titus Amba, ya bayyana cewa babu wani sabon ci gaba da aka samu biyo bayan jawabi ga ‘yan kasa da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi a yammacin ranar Litinin.
A wani labarin kuma, Jerin Sunayen Ministoci: Tinubu Bai Yi Kuskure Ba – Yari
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya gudanar da bincike mai zurfi a kan kowane daya daga cikin ministocin da ya nada.
Yari ya yi magana ne yayin da yake jaddada cewa majalisar dattawa na gudanar da cikakken tantance wadanda aka nada a matsayin ministoci, kamar yadda Daily Post ta rawaito.