Sadiq Aminu Wali, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano, ya sha alwashin zuwa kotun daukaka kara bayan wata babbar kotun tarayya da ke jihar ta kore shi.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa babbar kotun tarayya ta bayyana Mohammed Sani Abacha dan marigayi shugaban kasa, Janaral Sani Abacha a matsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano ranar Alhamis.
Hukuncin, wanda Alkalin Kotun, Mai shari’a A.M Liman ya yanke, an yanke shi ne ta hanyar zoom, inda ya umarci Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa, INEC da ta cire sunan Wali tare da maye gurbinsa da Abacha.
KU KARANTA KUMA Kotu Ta Kori Wali, Ta Tabbatar Da Abacha A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Na PDP
Daga nan ne kotun ta amince da zaben fidda gwani da bangaren Shehu Wada Sagagi ya gudanar a gidan Lugard, wanda ya gabatar da Abacha a kan zaben da bangaren Wali ya gudanar a cibiyar matasa ta Sani Abacha.
Wanda bai gamsu da hukuncin ba, Wali dan tsohon Ministan Harkokin Waje, Aminu Wali, ya ce zai dawo da matsayinsa a kotun daukaka kara.
Da yake magana da manema labarai a Kano a yammacin ranar Alhamis, Wali ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa lauyoyinsa na nazarin “hukunce-hukuncen da ke tattare da kura-kurai” a shirye-shiryen daukaka kara.
A cewar Wali, lauyoyinsa sun riga sun gano kurakurai da dama kan hukuncin, wanda zai ba shi kwakkwarar hujjar maido da abin da ya bayyana a matsayin “majibin mutanen Kano” a kotun daukaka kara.
Wali ya tuna cewa wani dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Ja’afar Sani Bello, ya maka shi kotu domin kalubalantar takararsa amma ya samu nasara a kotun daukaka karar.
Ya bayyana fatansa cewa “zamu yi nasara a kotun daukaka kara in Allah ya yarda. Za mu yi nasara kuma za mu yi nasara a zaben 2023 da yardar Allah.
“Wannan hukuncin yana cike da kurakurai amma saboda ni ba lauya ba ne, ba zan iya cewa komai kan wannan ba, amma lauyoyi na za su yi magana a kai,” in ji Wali.
A nasa bangaren, lauyan Wali, Nasir Adamu Aliyu (SAN) ya ce sun tattara fiye da dalilai ashirin na kariya a kotun daukaka kara.
A cewar Aliyu, Wali ya samu nasara a kotun daukaka kara a lokacin da Ja’afar Sani Bello ya shigar da kara yana kalubalantar zaben fidda gwani bayan da jam’iyyar PDP ta kasa ta gudanar da shi yadda ya kamata.
A Wani Labarin Kuma Gwamnan PDP Ya Gwangwaje ‘Yan Fanshon Jiharsa Da Kyautar N10,000 Na Kirsimeti
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Juma’a, ya amince da bayar da kyautar Naira 10,000 ga kowane dan fansho a jihar.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Taiwo Adisa, ya fitar, ya ce an dauki matakin ne domin taimakawa ma’aikatan da suka yi ritaya, wadanda suka yi wa jihar hidima da nagarta, don samun kyakkyawan Bikin kirsimeti.