Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Juma’a, ya amince da bayar da kyautar Naira 10,000 ga kowane dan fansho a jihar.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Taiwo Adisa, ya fitar, ya ce an dauki matakin ne domin taimakawa ma’aikatan da suka yi ritaya, wadanda suka yi wa jihar hidima da nagarta, don samun kyakkyawan Bikin kirsimeti.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Yiwa Manyan Hafsoshi 51 Ado Don Karfafa Yaki Da Rashin Tsaro
Kuɗin, a cewar sanarwar, na zuwa ne kwanaki bayan gwamnati ta biya albashin watan Disamba na 2022 ga ma’aikata da kuma fansho.
Gwamnatin ta kuma amince da biyan albashin watan13, wanda Makinde ya ce za a biya a cikin wannan lokacin ko kafin ranar 31 ga wata Disamba, 2022.
A cewarsa: “Gwamnan ya amince da biyan N10,000 ga duk ‘yan fansho a jihar a matsayin lamunin Kirsimeti, Yana da fa’ida ga duk masu karbar fansho.
“Alamar na zuwa ne kwanaki bayan gwamnatin jihar ta biya albashin watan Disamba na 2022 ga ma’aikata da ‘yan fansho.Kazalika gwamnan ya amince da biyan albashin watan 13, wanda ake sa ran za a biya a ko kafin ranar 31 ga watan Disamba, 2022.
“Gwamnan ya yi fatan duk wadanda suka yi ritaya za su ji dadin Kirsimeti.
“‘Yan Fanshon sun nuna godiya da taimakon da Maigirma Gwamna ya yi ga tsofaffi da ‘yan kasar mu da suka yi ritaya, wadanda suka yi wa jihar hidima mai inganci tsawon shekaru.”
A wani labarin kuma, Gwamna Masari Ya Nada Sanata Ida A Matsayin Sabon Shugaban Jami’ar UMYU
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya amince da nadin Sen. Ibrahim Ida, a matsayin sabon shugaban jami’ar, Umaru Musa Yar’adua UMYU mallakin gwamnatin Katsina.
Abdullahi Yar’adua, daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Muntari Lawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a Katsina.