Rahotanni na nuna cewa an cigaba da Gwabza fada a birnin Geneina dake yankin Darfur na kasar Sudan, inda akalla mutum fiye da Dari biyu suka mutu a karshen makon jiya.
Yayin gwabzawar a ranar Talatar data gabata an jiyo karar musayar wutar manyan makamai a yankin.
Ana dai cigaba da samun takun Saka tsakanin Larabawa makiyaya da Yan Kabilar Massalit wadanda ke cigaba da baiwa hammata iska na tsawon shekaru masu yawa.
Kana ko a ranar Lahadi Yan kungiyar Janjaweed dake samun goyan bayan rundunar Rapid Support sai da suka kaddamar mummunan hari a yankin na Geneina.
Birnin dai na tattare da dubban dubatan fararar hula wadanda suka gina gidaje tun bayan kaura da suka yi sanadiyar yaki a yankin Darfur shekaru fiye da 20 da suka gabata.
A wani labarin Kuma na daban anan gida Najriya.
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta musanta cewa akwai wata baraka a cikin shugabancinta biyo bayan amincewar da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP suka yi a matsayin ‘yan takarar da aka amince da su bisa tsarin yarjejeniya.
Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NEF, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, yayin da yake yin karin haske ga manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, ya bayyana cewa tsarin amincewar yarjejeniya ga jam’iyyar PDP ya samu albarkar shugabanta, Farfesa Ango Abdullahi.
A cewar Baba-Ahmed, “Abin da ya yi bisa yarjejeniya abu ne mai kyau. Abin da yake so ya yi a fili yake. Ya yi abin da ya yi a matsayinsa na Farfesa Ango Abdullahi ba a matsayinsa na mai kira ko shugaban kungiyar dattawan Arewa ba.”
Ya kuma bayyana cewa shugabancin kungiyar na goyon bayan Farfesa Ango Abdullahi kan yadda ya fito da ’yan takarar da suka amince da su bisa tsarin yarjejeniya a jam’iyyar PDP daga Arewa.
A cewarsa “Muna biyayya gareshi (Ango Abdullahi)”.
Tsohon Sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ya bayyana cewa ba sa adawa da Farfesa Ango Abdullahi, inda ya kara da cewa “ya jajirce wajen bin tsari da shugabanci na gari, don haka muna masa biyayya”.
Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na dandalin ya koka da cewa abin da kasar ke ciki a cikin shekarun da suka gabata shi ne saboda ‘yan Najeriya sun zabi shugabanni marasa galihu, yana mai cewa, “Ina ganin ba laifinsu ba ne, amma kuma laifinmu ne.”
Ya bayyana cewa wani abu ba daidai ba ne ga ’yan Najeriya, yana mai jaddada cewa “ba sa zaben shugabanni nagari wadanda suka damu da kasar, maimakon haka sai su zabi shugabannin da suka damu da kansu kawai.”