Rahotanni na nuni da cewa an sake lalata wutar lantarkin garin Maiduguri. Wanda hakan ya sake jefa birnin cikin duhu bayan kwana biyu da gyaran wutar bayan sun kwashe wata biyu babu wutar lantarkin sakamakon lalata wutar da Boko Haram suka yi.
Ofishin ministan lantarki na Nijeriya sun tabbatar da cewa an sake lalata wutar lantarkin, inda kasa da kwana guda ‘yan tada kayar baya suka sake lalata wasu turakun wutar lantarki biyu da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Ofishin ya wallafa haka ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce an dawo da wutar lantarki a Maiduguri babban birnin jihar Borno. Ya ce lalata turakun ya haifar da daukewar wuta a Maiduguri da kewayenta.
Ofishin ya ce a wannan karon ‘ya bindigar sun sanya bom ne akan turakun biyu wadanda aka lalata a baya kuma suka janyo dauke wuta ta kimanin watanni biyu a Maiduguri da kewayenta.
Sai dai kamfanin da ke samar da wutar a kasar ya ce za yi iya kokarinsa ya ga yadda za a gyara wannan barna a kan lokaci.