Wata budurwa ta fasa auren saurayin ta wanda suka kwashe shekara takwas suna tare bayan ya kwashe kuɗin da za a yi bikin auren su, ya sanya su a harkar caca, inda ya rasa su gabaɗaya.
Budurwar mai suna Linda ta bayyana hakan ne a wani shafin ƙulla alaƙar masoya a yanar gizo, inda ta ce ta ji daɗi zata kasance sa masoyin ta bayan shekara takwas amma caca ta lalata komai, shafin Yabaleftonline ya rahoto
KU KARANTA KUMA: Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Dokar Masarautun Jihar
A cewar budurwar ta san da cewa yana yin caca amm tayi tunanin cewa zai sauya, sai dai ta gane tayi kuskure lokacin da ya ƙi saurarawa kuɗin da za a yi bikin auren su ya zuba a harkar caca kuma ya zo ya rasa su gabaɗaya.
A kalamanta:
“Tabbas caca ita ta kawo ƙarshen soyayya ta masoyina ta shekara takwas. Ni budurwa ce, na yi zaton zai sauya, ya je yayi cacar kai tsaye da ake kira da “baby” da kuɗin da zamu shirya bikin auren mu kuma ya lalata su gabaɗaya, dole na ce na fasa auren”
Cacar zamani dai ta yanar gizo na ƙara zama ruwan dare a tsakanin matasan wannan zamanin.
Matasa da dama sun sha tafka asarar maƙudan kuɗaɗe a cikin harkar wacce idan aka fara tana da wuyar daina wa.
Abin Takaici: Bayan Kwashe Shekaru Tare, Magidanci Ya Gano ‘Ya’Yansa 2 Ba Na Shi Bane
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya shiga damuwa bayan gano cewa yaran sa 2 ba ƴaƴan sa bane.
Wani mutum mai suna Morris ya shiga cikin takaici bayan ya gano cewa ba shi bane mahaifin yaran sa guda biyu ba da matarsa ta ce ƴaƴan sa ne.
Mai shari’a Lauren Lake ta kotun US Paternity, itace ta bayyana hakan yayin da take yanke hukunci akan ƙarar Morris da matarsa,Thorpe, dangane da ƴaƴan su.