Wata lauya ta aje kwalin karatun ta gefe ɗaya ɗomin cika burin ta na zama mai gogaggiyar mai ɗinki.
Budurwar mai suna Maryam Folashade, ta bayyana ceea bayan ta kwashe shekara bakwai tana karatun zama lauya a jami’a, daga ƙarshe ta yanke shawarar to koma sana’ar ɗinki. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Sabon fim ɗin Shah Rukh Khan zai kafa wani sabon tarihi
A cikin bidiyon da ta sanya, an ga Maryam a cikin wani waje wanda yayi kama da shago. A cikin shagon akwai kekunan ɗinki da yawa.
Lokacin da ta shiga cikin shagon, cikin farin ciki ta zauna kan ɗaya daga cikin kekunan ɗinkin, kamar abinda ta daɗe tana jira kenan tayi a rayuwarta.
A ƙasan bidiyon ta rubuta cewa:
“Wata gaskiya dangane da rayuwata. Ni lauya ce mai son sana’ar ɗinki.”
Murna da farin cikin da ya bayyana a fuskarta ya nuna cewa wannan sgine abinda yake sanya ta farin ciki.
Ku kalli bidiyon a nan
Mutane da dama waɗanda suka bayyana ra’ayoyin su kan bidiyon ta, sun ƙarfafa mata guiwa inda suke cewa tayi abinda ya dace.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
Torlorunfe ta rubuta: ”
Bayan kwashe shekara biyar a makaranta, yanzu gyaran gashi nake koyo.”
@Ammy ta rubuta:
“Nima abinda nake shirin yi kenan.”
@user9966297060410 tayi tsokaci da cewa:
“Nayi karatun koyarwa yanzu ina gyaran gashi. Ba zamu taɓa saurarawa ba har sai mun kai inda muke so.”
@big baby beni ta rubuta:
“Mahaifiya ta tana jin cewa ni butulu ce saboda yadda nake maganar cewa ina son na kammala digiri ɗina na koma makarantar koyon ɗinki.”
Samari Da Dama Sun Bar Ni Da Raino Bayan Sun Ɗirka Min Ciki, Wata Budurwa Ta Koka
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koka kan yadda samari suka ci moriyarta sannan suka yada koronta.
Wata budurwa ta koka kan yadda maza daban-daban suka ɗirka mata ciki, suka gudu suka bar ta da rainon yara.
Budurwar mai shekara 23 a duniya ta bayyana cewa tana da yara uku yanzu haka, kuma kowanne daga cikin su mahaifin sa daban.
Budurwar ta dai bayyana wannan abin taƙaicin da ya faru da ita ne a wani bidiyo da ta sanya a manhajar TikTok.