Wani jariri mai shekara ɗaya Fabulous Michael Onwudiachi, an sace shi a ranar Alhamis da yamma a Jikwoyi a cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Raymond Onwudiachi mahaifin jaririyar, Ma’aikaci a Ma’aikatar Tsaro wanda aka sani da “Yankee Mouse” yace da misalin ƙarfe 2 a ranar Alhamis, ɗan shi mai shekaru 7 Famous, sun dawo da Makaranta Zuwa Shagon Mahaifiyar su a Jikwoyi, domin ɗaukar ƴar uwar su Fabulous, zuwa gidan Kakar su domin cin abincin rana, tsawon mita 10.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Sallami Mutumin Da Ake Zargi da kisan kai A Ekiti
A cewar Jaridar Vanguard, Onwudiachi yace suna wasa da ƴaƴen su da zarar sun dawo Makaranta, domin a kowane lokaci sukan so su ci abinci a gidan.
Ƴan mintuna kaɗan bayan sun bar gidan, sai suka dawo zuwa shagon Mahaifiyar dake yankin, inda suka bayyana cewa an sace ƙanen nasu.