By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Juma’ar da ta gabata ne birnin Kyiv ya bayar da rahoton cewa, an kai wani gagarumin hari ta yanar gizo kan wasu muhimman shafukan yanar gizo na gwamnati, a daidai lokacin da takaddamar da ke tsakanin Rasha da kasashen Yamma kan kasar Ukraine ta kara ta’azzara, biyo bayan tattaunawar da aka yi da dama da ba a yi nasara ba.
Ma’aikatar ilimi ta fada a shafin ta na Facebook cewa shafin yanar gizon ta ya lalace saboda ” hari na duniya (cyber)” da aka kai cikin dare.
Sauran gidajen yanar gizon da aka rushe sun hada da na majalisar ministoci da na ma’aikatun harkokin waje da na gaggawa.
Sai dai kuma babu wanda ya dauki alhakin kai harin nan take.
Gidan yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen ya nuna wani sako na dan lokaci a cikin yaren Ukraine, Rashanci da kuma Poland wanda ya nuna cewa harin na martani ne ga matakin Ukraine na goyon bayan kasashen yamma.
“Yan Ukrain! An share duk bayanan sirri na ku kuma ba su yiwuwa a maido da su. Duk wani bayani game da ku ya zama jama’a, ku ji tsoro kuma ku yi tsammanin mafi muni.”
“Wannan na baya ne, na yanzu da kuma nan gaba. Domin Volyn, OUN, UPA, Galitsia, Polesye da kuma ga wuraren tarihi, “in ji shi, yana nufin ƙungiyoyin masu kishin ƙasa da yankuna na Ukraine.
Ma’aikatar ilimi ta ce hukumomi – ciki har da hukumar tsaro ta SBU da kuma ‘yan sandan yanar gizo – suna kokarin shawo kan lamarin.
Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da takun-saka tsakanin Rasha da kasashen Yamma ke kara ta’azzara game da kasar Ukraine, wadda tsohuwar kasar Soviet ce mai dabara.
Kasashen Yamma sun zargi Rasha da jibge tankokin yaki da manyan bindigogi da kuma sojoji kusan 100,000 a kan iyakar gabashin Ukraine da yaki ya daidaita a makonnin baya-bayan nan, a wani matakin da kungiyar tsaro ta NATO ta ce na shirin kai hari. Moscow ta ce ba ta da wani shiri na mamaye Ukraine.
A wannan makon Amurka da kawayenta na kungiyar tsaro ta NATO sun tattauna da kasar Rasha a kokarin da suke na ganin an sassauta rikicin, amma duk shawarwarin guda uku da aka yi a Geneva, da Brussels da Vienna – bai yi nasara ba.
A jiya alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sergei Ryabkov ya ce Moscow ba ta ga wani dalili na gudanar da wani sabon zagaye na shawarwarin tsaro da kasashen yammacin duniya ba, sakamakon rashin samun ci gaba.