A ranar Litinin ne kasar Rwanda ta sake bude kan iyakarta da kasar Uganda bayan rufe wa na tsawon shekaru uku da ta yi, lamarin da ke nuni da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu na gabacin Afirka ya zo karshe.
An rufe iyakokin ne a watan Fabrairun 2019 yayin da takaddamar siyasa ke kara ruruwa tsakanin Kigali da Kampala, lamarin da ya kai ga kusan rugujewar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.
Kasar Rwanda ta sanar da matakin sake bude iyakar a makon da ya gabata a matsayin wani mataki na gyara alakar da ta yi tsami sakamakon zarge-zargen leken asiri da sace-sacen bayanai da kuma katsala Landan a harkokin cikin gida.
Hakan ya biyo bayan ziyarar da dan shugaban Uganda Yoweri Museveni, Muhoozi Kainerugaba ya kai Kigali, inda ya gana da shugaban Rwanda Paul Kagame.
An sake bude babban mashigin Gatuna da aka fi sani da Katuna a kasar Uganda a hukumance da tsakar dare, kuma ana sa ran zirga-zirgar z za ta rika tafiya a duk rana a dukkannin kasashen biyu.
Museveni da Kagame sun kasance aminan juna a shekarun 1980 da 1990 a lokacin gwagwarmayar neman madafun iko a kasashensu, amma dangantakar ta yi tsami daga bisani.
Rwanda ta rufe iyakokin ne bayan da ta zargi Uganda da sace ‘yan kasarta da kuma goyon bayan ‘yan tawayen da ke neman hambarar da Kagame daga kijeransa.