By Abbas Yakubu Yaura
Akalla ‘yan takara 127,491 da suka nemi shiga aikin ‘yan sanda daga ranar Talata za su mamaye hedikwatar ‘yan sandan jihohi domin a duba lafiyarsu.
Wadanda suka nema sun hada da mutane 104,403 daga yankin Arewa da kuma 23,088 daga Kudancin kasar nan.
Wani rahoto ya nuna cewa jihohin Abia na da masu neman aikin ‘yan sanda 596; Akwa Ibom 3,536; Anambra 314; Bayelsa 759; Cross River 2,704; Delta 976; Ebonyi 463; Edo 1,206; Ekiti 1,417; Enugu 707; Imo 852; Legas 562; Ogun 1,154; Ondo 2,472; Osun 2,006; Oyo 1,767 da Rivers 1,597.
Sauran sune jihar Plateau 4,100; Kebbi 3,596; Katsina 7,605; Kano 7,557; Kaduna 7,436; Jigawa 4,951; Benue 6,578; Adamawa 8,206; Bauchi 7,140; Borno 8,693; Babban Birnin Tarayya 4,418; Kogi 4,412; Kwara 2,410; Nasarawa 4,700; Neja 4,672; Sokoto 2,450; Taraba 4,075; Yobe 4,992; Gombe, 4,416 da Zamfara 1,990.
Saƙon kar takwana na wayoyin salula ya umurci masu nema su ci gaba da da bin umarnin ‘yan sanda wanda zai fara aiki daga ranar 1-20 ga watan Fabrairu.
An umurci masu nema da su bayyana tare da Lambar Shaidar katin dan Ƙasa na asali da kuma poto kwafi na takardun shaida, takaddun asali, takaddun haihuwa wadanda suke bayyana shekaru, bugu na aikace-aikacen da cikakkun takardun wanda ya tsaya maka wato (guarantor).
Sakon mai taken, ‘2021 daukar ‘yan sanda 10,000 aiki, ya shawarci jami’an da ke gudanar da atisayen da su tabbatar an ba da shawarar wadanda aka tantance kawai bisa cancanta.
Sannan hukumar tace a yi taka tsantsan game da ayyukan cin hanci da rashawa tare da gargadin jami’an da su bi ka’idojin da aka gindaya a cikin dokar ‘yan sanda.
“Dole ne ku tabbatar da cewa ofisoshin bincike na musamman da aka zaba suna nan a jihohi daban-daban da hedkwatar hukumar FCT da aka kebe a matsayin cibiyoyin motsa jiki, kafin, lokacin da kuma bayan tantancewar jiki.
“Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya kara da cewa, za su gudanar da bincike kan barazanar a cibiyoyinsu tare da bayyana duk wadanda aka gayyata domin kada a dauki masu aikata laifuka a cikin rundunar.
Shugaban ‘yan sandan ya kuma umurci mutanensa da su tabbatar an tantance ‘yan asalin jihar ne kawai, inda ya ce za a gudanar da tantancewar ne a kan kananan hukumomi.