Bazai taɓa yiwuwa Miyetti Allah ta ƙyale Ɗan gida, ta sayi Fom ga Goodluck Jonathan ba — Shehu Sani
Tsohon Sanatan Shiyyar Kaduna ta Tsakiya yace Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah MACBAN bata sayi Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa na Miliyan 100 ga Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jigawa: Ƴan Majalisu sun kori Shugaban Ƙaramar Hukuma kan Ƙin Biyayya ga Shugaban APC
A cewar sa, Ƙungiyar anyi amfani da’ita domin cimma muradun siyasa, yana mai mamakin yadda Ƙungiyar za ta ƙyale Ɗan uwan ta Alhaji Atiku Abubakar sannan ta saima Jonathan Fom ɗin Takara.
Idan dai ba’a manta ba, Jonathan yace shi bai cewa kowa ya sai mashi Fom ɗin Tsayawa Takara, kamar yadda Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah tayi.
Dayake maida jawabi Shehu Sani, ya jaddada cewa Ƙungiyar Miyetti Allah da bata sayi Tikitin Tsayawa Takara na Naira Miliyan 40 ga Fulani Atiku Abubakar, ba zata sayi na Naira Miliyan ga Goodluck Jonathan ba” .
Ya ƙara dacewa kawai ana amfani da sunan su ne domin cimma wani muradi na Siyasa.
Shehu Sani ya bayyana haka a wani sako daya saki a shafin sa na Twita.