By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis din data gabata ne wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka bindige wasu mutane bakwai ciki har da ‘yan kungiyar sa kai na al’umma a cikin wata mota da ake zargin ‘yan kungiyar masu aikata laifuka ne ta Azonto a Tor Donga dake karamar hukumar Katsina-Ala dake jihar Binuwai.
Har ila yau, harin ya yi sanadin mutuwar wasu mutane biyar da suka hada da Reverend Father daga unguwar Mbatseer, wadanda suka jikkata kuma a halin yanzu suna samun kulawa a wani asibitin gwamnati.
Da yake tabbatar da harin a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Juma’a, Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Mista Alfred Atera yace ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 5 na yamma.
Sannan yace “’Yan bindigan sun zo Tor Donga jiya da yamma inda suka kashe mutum bakwai.Sun kashe ‘yan kungiyar sa kai na al’umma, tare da raunata biyu daga cikinsu, sannan suka kashe wasu kuma a kan hanyarsu ta hanyar harbi da bindiga.
“Mutane biyar da suka jikkata a halin yanzu suna asibiti ciki har da wani Reverend Father daga unguwar Mbatseer dake zuwa Tor Donga. Sun same shi, suka harbe shi suka kashe wanda ke cikin motar tare da shi.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma.inda yace Su ne ragowar sojojin Azonto na ƙarshe a cewar memban Guard sun ga wani ma’aikaci dake tuka motar da suka shigo da ita.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An sanar da dukkan hukumomin tsaro, ‘Yan sanda, Operation Whirl Stroke, OPWS da mai baiwa Gwamna shawara kan tsaro duk an sanar dasu faruwar lamarin.
Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na ‘yan sanda, mataimakiyar Sufurtanda, DSP, Catherine Anene tace kawo yanzu “ba mu samu wannan rahoton ba don Allah.”