By Abbas Yakubu Yaura
Kasar Amurka ta yi alkawarin kara karfafa alaka da kasar Najeriya da sauran kasashen Afirka, inda ta bayyana cewa ba ta son takaita huldar da kasar ke yi da sauran kasashen.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya bayyana cewa kasarsa ba ta son tilastawa Najeriya zabi amma muna so mu ba ka zabi.
Blinken ya bayyana hakan ne a taron kungiyar ECOWAS dake gudana a Abuja ranar Juma’a, inda ya nuna adawa da koma bayan dangantakar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin wanda ya haifar da lamuni na biliyoyin daloli daga cibiyoyin hada-hadar kudi na kasar Sin da sauran yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya.
Sai dai babban jami’in na Amurka, wanda bai yi magana kai tsaye kan ikon yankin Asiya ba a cikin jawabin daya yi wa kungiyar kasashen yankin, ya bayyana bangarori biyar dake da moriya daya tsakanin Amurka da Afirka.
Wadannan, in ji shi, su ne kiwon lafiyar duniya, matsalar yanayi, da suka hada da bunkasar tattalin arziki, dimokuradiyya, da zaman lafiya da tsaro.
Sannan ya kuma bayyana goyon bayan Amurka ga yaki da cin hanci da rashawa da matakan bayyana ayyukan yi, don haka shugabanni da ‘yan kasa zasu iya tantance ko yarjejeniyar da aka yi a madadinsu ta cancanci hakan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Blinken yace “Muna kira ga gwamnatoci dasu bada gudummawar da kuma sadaukar da kai ga matakan shari’a na aikata laifuka da kuma hanyoyin tsaro dake mutunta hakki, da kuma yin la’akari da cin zarafi, wanda ke da mahimmanci don samun amincewar jama’a.
Kazalika yace “Muna tunanin za mu iya samun ingantaccen sakamako wajen fuskantar matsalar rashin tsaro idan har muka hada kai don fadada damar tattalin arziki, musamman ga matasa da sauran wadanda za su iya shiga cikin ayyukan muggan laifuka ta hanyar yanke kauna, saboda jin cewa basu da wani zabi.”