By Abbas Yakubu Yaura
Aloy Ejimakor, lauya na musamman ga Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, ya mayar da martani yayin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bada belin jagora masu fafutukar kafa kasar Biafra.
Ejimakor ya ce hukuncin da wata babbar kotun jihar Abia da ke zama a Umuahia ta yanke a baya-bayan nan zai yi tasiri kan hukuncin mai shari’a Binta Nyako.
Da yake magana da Jaridar DAILY POST, Lauyan na musamman ya ce hukuncin da kotun Umuahia ta jagoranta shi ne kawai dalilin da za a ci gaba kan hukuncin Abuja.
Idan zaku iya tuna cewa Mai Shari’a Nyako ya ki amincewa da bukatar bada belin Kanu a ranar Laraba.
Alkalin ya ce ya kamata Kanu ya bayyana inda ya ke a lokacin da ya tsallake beli a shekarar 2017.
Da yake mayar da martani Ejimakor ya ce: “Mai shari’a ta ki amincewa da bukatar belin, amma ta kuma yanke hukuncin cewa Kanu zai iya sake neman belin tare da bayyana dalilin da ya sa bai halarci kotu ba a shekarar 2017. A nan ne hukuncin Umuahia zai fara aiki.
“An shigar da bukatar beli na farko (wanda aka ki a yau) a gaban hukuncin Umuahia wanda ke nuni da wanke Kanu daga ra’ayin cewa ya tsallake beli a shekarar 2017.
“Mahimmanci sosai. Shi ne kawai tushen da sabon neman belin zai iya ci gaba da kasancewa. “
Comments 1