Shugaba Joe Biden ya nada Richard Mills, Jr a matsayin sabon jakadan Amurka a Najeriya.
Fadar White House ta sanar da hakan.
Sanarwar ta ce Richard Mills, Jr zai yi aiki a da kwarewarsa na shugaban a gwamnatin Biden.
Mills, Jr. a halin yanzu yana aiki a matsayin Mataimakin Wakilin Dindindin na Amurka a Majalisar Dinkin Duniya kuma memba na Babban Ma’aikatar Harkokin Waje tare da mukamin Mai ba da shawara.
Kafin nadin nasa, Mista Mills ya taba zama jakadan Amurka a kasar Armeniya. Ya kuma kasance a matsayin bababn Mataimakin Shugaban Ofishin Jakadancin sannan kuma yayi aiki a Ofishin Jakadancin Amurka dake kasar Kanada.
Sabon wanda aka zaba a matsayin jakadan Amurka a Najeriya ya kuma taba zama mataimakin jakadan Amurka a birnin Beirut na kasar Lebanon da kuma mataimakin shugaban ofishin jakadanci kuma mai kula da harkokin kasashen waje a Ofishin Jakadancin Amurka na birnin Valetta dake kasar Malta.
Mista Mills, dan asalin jihar Louisiana, kafin ya shiga Ma’aikatar Harkokin Waje, ya kasance Mataimakin Lauya tare da kamfanin Duncan, Allen da Mitchell a Washington, D.C.
A wani labarin kuma na daban.
Al’ummar jihar Kano sun fara mayar da martani kan sabuwar dokar da gwamnatin Kano ta ayyana, na dakatar da zirga zirga baburan adaidaita sahu daga karfe 10 na dare.
A martanin su daban daban, yayin ganawar su da JARIDAR DIMOKURAƊIYYA, wasu sun yi na’am da wannan tsari, yayin da wasu ke Allah wadai.
Dokar dai zata fara aiki ne daga ranar 21 ga watan nan na Yuli, daga 10 ma dare zuwa 6 na safe.
Ga ra’ayoyin wasu Kanawan kamar haka:
Ni sunana Usman Kabeer, ”maganar gaskiyar wannan mataki yayi daidai, saboda yanzu yadda harkar adaidaita sahu ta lalace sai da hakan.”
Auwal Ishaq, ”wannan abun muka dade muna rokon ayi mana, amma sai yanzu Allah ya nufa, don haka dari bisa dari ina goyon bayan, kai idan da ace zan bada shawara a mayar da dokar ta koma karfe 8 ma dare maimakon 10pm.”
Khadija Abdulwahab, ”gaskiya wannan ba itace mafita ba, saboda yawancin masu sana’ar nan basu me mutanan banza ba, na ba zan ƙalilan ne.”
Mustapha Jibril, ”haba malam wannan kawai barin jaki ne, a koma dukan tanki, shin an samar mana da abubuwan da zamu dinga biya don zirga zirga bayan goman daren?, Maganar gaskiya idan akai haka ba adalci a cikin wannan batu.”
Lawandy G, ”yanzu dai kaga ni dan kasuwa ne ta kauye, ina naje kasuwa ina dawowa nan Kano wajen 11 ko 12 saura, yanzu yaya ake so muyi ke nan?.”
Gwamnatin Kano dai a ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba, ya ce wannan mataki ana fatan zai kawo sauyin ga matsalar da ake fuskanta daga matuka baburan adaidaita sahun.