An samu hargitsi a wajen wani bikin aure bayan kwatsam kawai amarya ta kama dukan ango a wajen bikin su a ƙasar Rwanda.
Bidiyon da aka ɗauka a wajen bikin ya nuna lokacin da ango da amarya suka fito daga wani katafaren gida suka nufi coci domin a ɗaura aure. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Matar data turo maƙudan kuɗaɗe daga ƙasar, ta dawo ta tarar ɗiyarta tayi bushasha da su
Su biyun suna riƙe da hannun juna yayin da amaryar kuma ta riƙe fulawa a hannunta. Kwatsam kawai sai ta saki hannun angon ta kama shi da duka.
Daga nan sai tayi watsi da fulawar gefe ɗaya ta fara shirin yin faɗa, yayin da ƙawayen ango dana amarya suka rugo domin shiga tsakani.
Babban abokin ango da ƙawayen amarya sun samu sun riƙeta yayin da take ƙoƙarin ƙara dukan ango.
Sun matuƙar wahala wajen riƙe amaryar wacce take a cikin fushi, inda daga bisani ta faɗi a ƙasa. Wasu daga cikin ƙawayen amarya har kuka suka riƙa yi.
Ga bidiyon nan ƙasa:
CBN Ya Gargadi Bankuna Kan Sa Tsoffin Kudi A Na’urar ATM
A wani labarin na daban kuma, babban bankin Najeriya yayi gargaɗi kan bankunan dake sanya tsofaffin kuɗi a wajen ciro kuɗaɗe
Babban bankin Najeriya, CBN, ya yi gargadin illar da bankunan kasuwanci za su fuskanta idan aka samu suna sanya tsofaffin katunan kudi a ATM dinsu kafin ranar 31 ga watan Janairu.
Da take magana a ranar Alhamis a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, a lokacin da ake wayar da kan ‘yan kasuwa game da sake fasalin kudin naira, mataimakiyar darakta a hukumar kula da kudaden, Dr Rekiyat Yusuf, ta ce duk wani ATM da aka samu har yanzu an saka masa tsofaffin takardun kudi za a rufe shi kuma a sanya masa takunkumin da ya dace a bankin aiki.