Wata matashiya ƴar Najeriya ta bayyana maƙudan kuɗaɗen da take biya a matsayin kuɗin haya a wani tsibiri ciki. jihar Legas.
Matar ta gayawa wani mai amfani @walesmorgan a TikTok, yawan maƙudan kuɗaɗen da take biya a cikin wani bidiyo. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Abun al’ajabi: Tagwaye sun samu juna biyu a tare, sun haihu lokaci ɗaya
Matashiyar dai tana daga cikin mutanen da suka amsa tambayar jin daga bakin mai ita kan kuɗin hayar da suke biya.
Bayan ta gaya masa cewa tana biyan Naira dubu ɗari takwas (N800,000) a duk shekara, ta zagaya da shi cikin gidan domin nuna masa yadda yake.
A cikin bidiyon ta nuna masa kayayyakin cikin gidan da yadda aka tsara su da kuma wasu daga cikin abubuwan da tafi alfahari su.
Matashiyar ta kuma bayyana cewa gidan na ta na musamman ba kamar sauran gidaje ba domin ko kaɗan ba a ɗauke wutar lantarki a gidan.
A ƙarshen bidiyon ta ba mutumin abinci mai ɗan karen daɗi domin ya mayar da yawun sa.
Ku kalli bidiyon a nan
Sinzah ya rubuta:
“Dan Allah a wace unguwa take zama, dubu ɗari kan wannan gidan ai yayi.”
Oluchi ta rubuta:
“Lol daga zagaya gida ka koma cika ƙundu.”
nero ya rubuta:
“Wannan matashiyar tayi gaskiya.”
King coco ya rubuta:
“Tana da kirki. Ta tambaye shi ko yana jin yunwa, ba kowa bane yake fahimtar mutane na son cika ƙundun su ba.”
Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da NNPP Ta Shigar Domin Kalubalantar Uba Sani
A wani labarin na daban kuma, kotu tayi fatali da ƙarar da jam’iyyar NNPP ta shigar akan ɗan takarar gwamnan APC.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna a ranar Larabar ta yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP ta shigar kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Jam’iyyar APC da dan takararta na Gwamna Uba Sani.
Lauyan Jam’iyyar APC reshen Jihar Kaduna kuma tsohon Shugaban Hukumar NBA a Jihar, Sule Shu’aibu a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: