Wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 14 ya nuna wani shugaban makaranta yana tiƙar rawa a gaban ɗalibai.
Shugaban makarantar ya tiƙi rawar sa a gaban ɗalibai waɗanda suka riƙa ihu suna yaba masa ciki da annashuwa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Wata Sabuwa: Yadda wani mutum ya rasa ransa daga rabon faɗa
Mutumin yana sanye sa riga mai kalar kore wacce akayi zanzaro da ita cikin baƙin wando haɗe da baƙin takalmi domin wankan ya hau iya hawa. Yana tsaye ne dai a sama yayin da ake taro da daliɓai.
Nan da nan kawai sai ya fara tiƙar rawa abinsa. Ya ɗaga ƙafars ta dama daga nan ya ɗaga ƙafarsa ta hagu kafin ya cigaba da kai kawo yana tiƙar rawa.
Yanayin rawar sa akwai ban dariya wanda ya sanya duk mutanen dake a wajen suka fara ihu suna yaba masa.
Malaman makarantar dake a wajen a tare da shi rawar sa tayi matuƙar burge su. Ɗaliban sun cika da annashuwa sosai inda har wasu daga cikin su suka fara karkaɗa jikin su.
Ba a san takamaiman dalilin da ya sanya shi wannna farin cikin ba, amma shugaban makarantar yana cikin murna saboda aukuwar wani abu.
@samusa91 shine wanda ya sanya bidiyon a manhajar TikTok.
Ku kalli bidiyon a nan
Allah Mai Iko: Bayan kwashe shekara 20 tana jiran haihuwa, wata matar aure ta haifi tagwaye
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta haifi tagwaye bayan ta kwashe shekara ashirin tana jiran haihuwa bata samu ba.
Wata matar aure ƴar Najeriya na cike da matuƙar farin ciki na samun tagwaye bayan ta kwashe shekara ashirin tana jiran samun haihuwa.
Matar auren yanzu haka na cike da tsananin farin ciki bisa wannan abin arziƙin da ya samu ahalin ta.
An sanya hotunan matar da na tagwayen ta a Facebook inda mutane da dama suka yi ta taya ta murna.
Tuni mutane da dama suka fara taya matar murna inda suma garzaya wajen yin sharhi domin yin fatan alkhairi ga jariran.