Wani magidanci ya zama abin magana bayan bayyanar bidiyon sa ya zakaɗe yana tuƙa tuwo.
Yanayin yadda magidanci ya dage yana tuƙa abincin ya sanya har zufa nata keto masa babu ƙaƙƙautawa.
Wani ɓangare na rigar sa har jiƙewa yayi sharkaf yayin da yake ta tuƙa tuwon a cikin tsakar rana. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA: Yadda dambe ya kacame tsakanin ango da amaryarsa ranar ɗaurin auren su
Daga ganin yadda mutumin yake sarrafa muciyar ya nuna cewa wannan ba shine karon farko da ya fara tuƙa tuwon ba.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su ta hanyar yaba masa bisa wannan namijin ƙoƙarin da yayi.
Wasu ƴanmata daga ciki har nunawa suka yi ya tafi da zuciyoyin su inda suka bayyana a matsayin irin mazan da yakamata mace ta aura.
Bidiyon dai ya karaɗe manhajar TikTok inda har sama da mutum dubu shida da ɗari tara suka danna alamar so akan sa wanda wani mai amfani da @user4118480046733 ya sanya.
@adamandaratu795 ya rubuta:
“Kayi komai ɗan’uwana. Zan baka kyauta a ƙarshen shekarar nan.”
@Nana Owusu korkor ta rubuta:
“Wannan shine cikakken namiji.”
@Samson Yohanna400 ya rubuta:
“Aiki mai kyau ɗan’uwa.”
Rashin Miji Na Damuna, Na ƙosa Nayi Aure -Kyakkyawar Budurwa Ta Koka
A wani labarin na daban wata budurwa ta koka saboda rashin mijin aure, tace ta gaji da zama hakanan.
Wata kyakkyawar budurwa ƴar Najeriya ta koka a kafafen sada zumunta kan yadda har yanzu bata samu mijin aure ba.
Kyakkyawar budurwar wacce ke amfani da sunan Chris Amrah a manhajar TikTok, ta sanya wani bidiyo inda take cewa ta gaji matuƙa da zama babu miji sannan ta ƙosa tayi aure domin ta ji abinda ake ji a rayuwar aure.
A cewar ta, ta ji abubuwa da dama akan aure, masu kyau da marasa kyau, amma duk da hakan tana son ta ji ya ake ji idan anyi aure da kuma zama a ƙarkashin ikon mijinta.