Kungiyar Matasan Arewa ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta dakatar da Shirin wasan kwai-kwayo na Big Brother Naija.
Kungiyar ta bayyana Shirin wasan kwai-kwayo a matsayin wata Masifa da ku wata dabi’a mai lalata tarbiyar al’um, wanda ta ce, a kwai bukatar dakile shi.
Shugaban kungiyar na Kasa Yerima Shettima ne ya yi wannan kiran a hirarsa da manema labarai a yau Asabar.
Shettima ya ce, Fim din na kama da fina-finan batsa, inda ya ce, mutane da dama na kwallon fim dinne domin koyar wata dabi’ar banza.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ngige ya Gargadi Likitoci kan shiga yajin aiki
Ya ce, ” Fim din ban ta ba yadda da shi ba, Kuma banga alamar ya da ce a bar fim din ya cigaba ba, domin ya na lalata tarbiyar al’uma ne kawai” inji shi.
“Nasha nanata wa, Shirin na lalata tarbiya, kuma ya kamata Gwamnatin Nigeria ta dakatar da shirin, domin bai kamata ace a kyale shi ba, ana cigaba da yadashi a cikin kasar mu” a cewar shi.
“Kuna ganin yadda mutane da dama ke kallon fim din, domin koyan dabi’ar banza, domin anayin Shirin fim din ne kamar fim din batsa”
“Don haka ina rokon masoya kasar nan na hakika, da mu hada hannu, wurin janyo hankalin Gwamnati dangane da illar dake tattare da wannan fim, wanda ya kamata a dakatar da shi” inji shi.