Ministan Kwadago na kasa Chris Ngige y ya ja kunnen kungiyar likitoci da kada su kuskura su shiga wannan yajin aikin da ake yi wanda ya kira da “Rashin hankali”.
jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa, ta shiga yajin aiki ne, bisa zargin gwamnatin tarayya da karya yarjejeniyar da suka yi da kungiyar tun a baya.
Kokarin da gwamnatin take yi na ganin cewa likitocin sun janye yajin aikin da suka fada ya gagara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zahra Bayero ba ta fi karfin doka ba, inji Hukumar Hisbah
A mako mai zuwa zan tada wannan al’amarin saboda sasanci ya ki aiki. Ba zan sake ganawa dasu ba saboda ina da abubuwan yi.
Kazalika ya ce, Sasanci biyu nayi jiya, zan cigaba da bata lokacina a kansu ne? Ina da wasu mafita a cikin dokokin kwadago kuma zan yi amfani dasu.
Zan yi amfani da sashi na 43. Na sanar da kungiyar ba zasu samu albashi ba a yayin da suke yajin aiki, kuma ba zai taba shiga cikin tarinsu na fansho ba.
A wani labarin Kuma.
Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Nigeria ta bayyana cewa, adadin wadanda suke fama da cutar Covid-19 na kara bazuwa, a yayinda mutane Dubu 9, 066 suke fama da cutar, gami da Karin mutane 565 a ranar Juma’a.
Hukumar ta bayyana hakan a Shafin ta na yanar gizo a ranar Asabar da Safe.
Kamfanin Dillancin Labaru na Kasa ya ruwaito cewa, yawan masu kamuwa da cutar, ya nuna karuwa dlzuwa Dubu 9,033.
Hukumar tace mutane 76 sun warke daga cutar, an kuma sallame su daga cibiyoyin masu kula da cutar a ranar Juma’a a Kasar.
Hukumar kula da Lafiyar Al’umma tace kafin yanzu, wadanda suka kamu da cutar Dubu Dari 165,409 sun warke a Jahohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Acewar ta, Wadanda suka kamu a ranar Juma’a, an samu mutanen ne a Jahohi 16 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kamar yadda bayanan Hukumar NCDC ya bayyana, Jahar Lagos tafi kowacce jaha, yawan wadanda suka kamu da mutane 348, sai Rivers guda 70, a yayinda Akwa Ibom yakai mutane 45 da sauran su.