Gwamnatin jihar Kano yayi afuwa ga Ɗaurarru 90 da suke tsare a gidajen gyaran hali na Jihar Kano.
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci yi musu afuwar, a wani bangare na murnar bikin sallah Ƙarama, inda ya bukace su da suyi amfani da damar wajen zama mutane na gari da kuma kaucewa duk wani abu da ka iya jawo musu komawa wannan gida.
Kazalika ya kuma yi Albashir din cewa zai sake yiwa wasu afuwa nan da zuwa kwanaki 70 wato lokacin Idin babbar Sallah.
Gwamnan ya bayyana hakan a yau Litinin lokacin da ya ziyarci gidan gyaran hali na Goron Dutse, tare da rakiyar tawagar jami’an gwamnatin jihar, da kuma shugabannin jam’iyyar APC.
Ya ce afuwar da aka yi musu ba ya nufin domin rage cunkoso bane, illa domin sake basu damar zama mutane na gari, bayan daukar darasin rayuwa a gidan gyaran halin.