Kungiyar Kwadago reshen jihar Kano ta sanar da kudurinta na marawa uwar kungiyar ta kasa baya, wajen zanga-zangar adawa da Yajin aikin kungiyar ASUU.
Shugaban kungiyar Kwadagon reshen Kano Kwamared Kabiru Ado Munjibir ne ya sanar da hakan, yayin bikin Ranar ma’aikata ta duniya ta shekarar 2022.
Ya kuma godewa daukacin ma’aikatan jihar Kano bisa jajircewar da suke nunawa wajen ganin an samar da ci gaba mai dorewa a jihar Kano baki daya.
Da yake tabo batun Rage albashin ma’aikata kuwa, Kwamared Munjibir ya ce ma’aikata su kara hakuri, sakamakon yadda tattalin arzikin duniya ke ci gaba da fuskantar koma baya.
A cewar sa hakan ya tilastawa gwamnati daukar matakin zaftare albashin ma’aikatan na wasu yan watanni, kuma a cewar sa zasu ci gaba da kokari matsayin na kungiya wajen ganin gwamnati ta dawo da kudin da ta zaftare musu, bayan al’amura sun daidaita.
A karshe ya ce zasu gudanar da zanga-zangar matakin kasa domin jawo hankalin gwamnati wajen ganin ta magance matsalar da kungiyar malaman jami’o’in ASUU ke fuskanta, wanda suka tilasta musu tafiya aiki.