Gwammanatin Birtaniya ta biya diyyar mutuwar mutane da suka rasa rayukansu A Afghanistan wanda ya zarce yawan yaran da suka rasa rayukansu a ƙasar da kusan sau huɗu. Kamar yadda BBC ta ruwaito
Gwamnatin kasar ta bayar da diyyar ne ta mutuwar yara 64 , adadin da ya zarce mutum 16 ɗin da ta bayyana ta amince da su.
KARANTA WANNAN LAABRIN: Babu Wanda Ya Kai wa Atiku Hari A Borno – APC
Dukkanin su sun rasa rayukansu ne sanadiyar yaƙin da sojojin Birtaniya suka fafata daga shekarar 2006 zuwa 2014.
Sabbin alƙalumman sun fito ne daga bayanan kare haƙƙin bil’adama da ƙungiyar bayar da agaji a ɓangaren tashe tashen hankali da ya shafi sojoji wato action on Armed Violence (AOAV) ta nema.
Hare haren Jiragen sama na ɗaya daga cikin abubuwan da suka yi sanadiyyar mutuwar Mutanen.
Ƙungiyar bayar da agajin (AOAV) ta yi ammana cewa alkuman waɗanda suka rasa rayukansu sanadiyar haren haren na sojojin Birtaniya ya zarce adadin da aka bayyana.
Of those deaths that have been recorded, the actual number of children killed could actually be as high as 135, because some of the fatalities are described in Ministry of Defence (MoD)
Ƙungiyar tace yawan ƙananan yaran da suka mutu ya zarce 135, saboda a kwai wasu da lamarin ya shafa kamar yadda Maaikatar tsaro ta bayyana.
Kuñgiyar ta cigaba da cewa akwai yiyuwar daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai manya, mai yiyuwar shakarun sun kai 18 duba da yanayin shekaru a Afghanistan
Birtaniya dai tayi watsi da mafi yawan zarge-zargen kisan da aka gabatar mata, Inda daga cikin zargi 881 da aka yi wa Burtaniya tayi watsi da su, kashi ɗaya cikin huɗu ne kawai suka sami diyyar.
A gefe ɗaya bayanai ‘Yancin na baya bayan nan sun nuna yadda Burtaniya ke biyan kuɗin da ake kashewa a Afghanistan yana da ban banci sosai.
Bayanan sun nuna cewa a wasu lokuta, mutane sun fi samun diyyar akan asarar dukiya ko dabbobi fiye da ’yan uwansu da suka rasa.
Wata sanarwa, yarjejeniyar fahimtar juna da aka fitar tanuna cewa Duk wata mutuwar farar hular da aka samu yayin rikici, abin takaici ne da nuna damuwa fiye da halin da yara da ‘yan uwa za shiga ciki.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da na bayar da agaji sun sha sukar ƙasashen Amurka da Birtaniya kan yadda suke gudanar da bincike da kuma bayar da rahoton hasarar fararen hula a ayyukan Sojin ƙasashen.
A WANI LABARIN KUMA: PDP Ta Sauya Ranar Da Atiku Zai Yu Yakin Neman Zabe A Jihar Kebbi
Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake dage ziyarar yakin neman zaben ta a jihar Kebbi.
Jam’iyyar ta ce dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai ziyarci jihar ce a ranar 28 ga watan Janairu, kamar yadda NAN ta ruwaito