Birtaniya ta bukaci gaggauta sakin hambararren shugaban Nijar, Bazoum
Birtaniya ta yi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai a ofishin jakadancin Burtaniya, Atinuke Akande-Alegbe ya fitar a ranar Laraba, Burtaniya ta yi Allah wadai da tsare Bazoum ba bisa ka’ida ba da sojoji suka yi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Katsina Ta Musanta Batun Turo Mata Biliyan 5 Daga Gwamnatin Tarayya
Janar Abdourahamane Tchiani ya jagoranci sojojin da suka hambarar da gwamnatin kasar a ranar 26 ga watan Yuli, kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta sha alwashin mamaye kasar Nijar matukar gwamnatin mulkin sojan kasar ta kasa maido da tsarin dimokaradiyya tare da sakin Bazoum.
Da take magana game da juyin mulkin, Burtaniya ta ce, “Muna tare da ECOWAS domin yin Allah wadai da tsare shugaban Mohamed Bazoum, da iyalansa, da kuma wasu jami’an gwamnati ba bisa ka’ida ba, da kuma yanayin da ba za a amince da su ba da ake tsare da su, tare da yin kira nan take a sake su.”
A cewar sanarwar, Birtaniya ta amince da yunkurin diflomasiyya da Najeriya ke yi na maido da dimokuradiyya a Nijar, ta hanyar kasancewarta mambobin kungiyar ECOWAS, tare da yin Allah wadai da juyin mulkin da aka yi wa zababbun shugabannin Nijar.
Sanarwar ta bayyana cewa Ministan Sojin Birtaniya James Heappey MP a ranar Laraba ya gana da shugabannin tsaron Najeriya da hafsoshin sojin kasar domin tattauna halin da ake ciki a Nijar.
Har ila yau ya gana da shugaban hukumar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), inda ya jaddada goyon bayan Birtaniya ga kokarin da ECOWAS ke yi na tabbatar da dawowar dimokradiyyar Nijar cikin lumana.
“Rundunar sojin Birtaniya da Najeriya na da dadadden hadin gwiwa ta yadda za mu ci gaba da magance ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a yammacin Afirka da mashigin tekun Guinea.
Heappey ya ce “Birtaniya tana goyon bayan ECOWAS wajen yin kira da a maido da tsarin tsarin mulki da dimokiradiyya cikin lumana a Nijar kuma za mu yi aiki tare da ECOWAS da sauran takwarorinmu na yammacin Afirka don tallafa musu a wannan manufar,” in ji Heappey.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Osun Na Kokawa Kan Rashin Turo Mata Biliyan 5 Daga Gwamnatin Tarayya
A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin jihar Osun ta bayyana cewa har yanzu tana sa ran gwamnatin tarayya ta turo mata N5bn da ta yi alkawarin samar wa jihar domin dakile illar cire tallafin.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin da aka kafa don rabon kayayyakin tallafin shinkafar ya bayyana cewa, ya yanke shawarar jira kaso na biyu kafin a raba shinkafar ga marasa galihu.