- Bola Ahmed Tinubu ya kafa tarihin gwamnatin da ta fi kowace yawan ministocin tarayya a tarihin Najeriya
- Ministocin guɗu a 48 za su yi aiki da shugaban kasar, kowanensu ya na da albashi mai tsoka a kowane wata
- A cikin shekaru huɗu, babu mamaki gwamnatin APC mai-ci tayi barnar abin da ya zarce N8bn
Nan da shekaru huu masu zuwa, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta kashe kudin da ya zarce Naira biliyan takwas a kan ministocin tarayya.
Wani bincike da Daily Trust ta gudanar, ya nuna Najeriya za ta batar da Naira biliyan 8.63 domin biyan albashi, alawus da duk sauran haƙƙokin ministocin.
Abin bai tsaya a nan ba, ana zargin kudin zai iya karuwa idan har hukumar RMAFC ta yi wa masu rike da mukamai karin albashi a kan abin da su ke karba a baya.
Hakan ya nuna tufka da warwarar shugaba Bola Tinubu mai kokarin rage facaka da dukiyar al’umma, ana fito da tsare-tsare domin rage radadin talauci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ban Taɓa Rokon Kujerar Minista Ba – Inji Wani Sabon Ministan Tinubu
Rahoton ya tabbatar da cewa ministocin wanda suma za su nada ma su taimaka musu barkatai, za su sake jefa tattalin arziki cikin matsala, a rika batar da miliyoyi a duk wata.
Abin da za a kashe a wajen biyan albashi ga ministocin zai laƙume wa gwamnatin tarayya Naira biliyan 13. A haka ba a hada da manyan alawus da su ke ci ba.
Dalar Amurka za ta kara karyewa Sa’ilin da minista da mukarrabansa su ka bar Najeriya zuwa kasar waje, ana biyansu alawus a kudin ketare, hakan zai iya taimakawa wajen tashin Dala.
Hukumar RMFAC ta tsaida albashin minista a kowane wata a kan N650,135.99, a kowace shekara minista guda zai karbi N7.8m daga hannun gwamnati.
Daga cikin kudin akwai N1,519,800 domin hawa mota, N506,600 na sallamar mukarrabai, N1,519,800 domin barori sai kuma N911,880 na shakatawa.
Doka ta ba minista damar kashe N303,960 da sunan sayen jaridu. Bayan haka akwai kudin kama hayar gida, sayen kayan daki da motoci da kudin hutu. Hakan ya nuna a shekaru hudu, ministocin da za su yi aiki da gwamnatin Tinubu za su laƙume Naira Biliyan 1.497 a duk wata inda a shekara hudu za su tashi da Naira Miliyan 31.2.
Akwai wani karin alawus na N37.28m da ake biyan ministoci, hakan zai bada damar kashe masu N1.785bn a shekara, za su batar da N7.142bn nan da 2027.
Ministoci 48 a FEC A tarihi, tun daga Muhammadu Buhari, Goodluck Jonathan da Umar Yar’Adua, ba a taba samun lokacin da shugaban kasa ya rantsar da ministoci 45 ba.