Hukumar Kula da ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa ta yi kakkausan gargadi game da yaɗuwar mayukan bleaching “mai haɗari” da “marasa kayyadewa” a kasuwa, kamar yadda Punch ta rawaito.
Hukumar ta yi gargadi game da hadarin ne a ranar Laraba a wani taron bita na yini daya da ta shirya wa masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai a jihar Enugu mai taken, “Hatsarin man bleaching dake sanya hasken fata da kuma ka’idoji na doka.”
KARANTA WANNAN LABARIN: NAFDAC Tayi Gargadi Da Babbar Murya Kan Ci-gaba Da Amfani Da Man Bleaching
Da take gabatar da jawabi a wajen kaddamar da taron bitar, Darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, wacce ta wakilci daraktan tantance sinadarai da bincike, Dr. Patrick Omokpariola, ta bayyana cewa, “Ya zama wajibi a gare ni in yi gargadin cewa wasu illolin da ke tattare da man kara hasken fata na bleaching sun hada da ciwon daji, lalacewar gabobin jiki, kumburin fata da rashin lafiyan jiki, konewar fata da rabe-rabe, kurajen fuska, tsufan fata da kuma tsawaita warkewar raunuka”.
Adeyeye ta bukaci matan Najeriya da su yi alfahari da launin fatarsu, tana mai cewa, “Babu bukatar yin bleaching don su kara hasken fatar su duba da yanayin kyawun da suke dashi.”
Ta ce, “Binciken da hukumar lafiya ta duniya ta gudanar a shekarar 2018 ya nuna cewa amfani da man shafawa na fata ya zama ruwan dare a tsakanin kashi 77 cikin 100 na matan Najeriya, wanda ya kasance mafi girma a Afirka idan aka kwatanta da kashi 59 a Togo, kashi 35 a Afirka ta Kudu da kuma kashi 27 cikin 100. a cikin matan Senegal.
Wannan kididdigar mai ban tsoro ta nuna cewa barazanar man bleaching a Najeriya ya zama gaggawa na kiwon lafiya na kasa da ke buƙatar tsarin mai fuskoki da yawa, Wani bangare na tsarin da ya dace shine tarukan tuntuba/tarukan wayar da kan jama’a irin wannan da kuma kara kai hare-hare kan wuraren rarraba mayukan bleaching.”
Sai dai DG ta yi nuni da cewa taron wayar da kan jama’a ya kasance cika alkawarin da ta yi na ruguza shi zuwa shiyyoyin siyasa guda shida na kasar nan a matsayin dabarar wayar da kan jama’a da kuma kalubalantar ‘yan jaridan lafiya na Najeriya da su taka rawar gani a gaba a kokarinsu na ganin an kawar da matsalar man shafawa na Bleaching da kuma almubazzaranci da rashin bukata a Najeriya.
A wani labarin kuma, Kano: ‘Yan Sanda Sun Sake Jaddada Dokar Hana Hawa Keke Napep, Da Kilisa
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce dokar hana zirga-zirgar babura a fadin jihar daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe har yanzu tana ci gaba da aiki, inda ta yi kira ga masu hawan doki da su bi wannan umarni. Kamar yadda Daily Trust ta euwaito.
Rundunar ta kuma haramta hawan dokin gargajiya da aka fi sani da Kilisa a cikin watan Ramadan da kuma amfani da wasan wuta a cikin babban birnin jihar.