A jiya Laraba ce wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari garin Gujba na jihar Yobe.
Wani dan kungiyar ‘yan banga a yankin mai suna Mohammed Musa, ya ce maharan sun mamaye garin ne ta bangaren kudu ba tare da harbi ko daya ba.
Ya ce maharan a cikin ayarin motocinsu da karfin tsiya sun shiga wani asibiti tare da kwashe wasu kwayoyin magani.
Wani ganau daga asibitin, Kuma ya tsallake Rijiya da ba’a a Harin, kana ya nemi a sakaya sunanshi ya ce, maharan sun bi su har cikin asibitin, tare da kona motar daukar marasa lafiya ta asibitin.
Kazalika ya Kuma bayyana cewa, jami’an tsaro sun isa wurin ne bayan maharan sun bar wurin.
Har izuwa hada wannan rahoton, Manema labarai ba su Sami damar Ji ta bakin Kakakin rundunar Sojin ta Sashen II, Operation Hadin Kai a Damaturu, Laftanar Kennedy Anyewau ba.