Boko Haram ta kashe Mayaƙan ISWAP 6, a wani rikici daya ɓarke tsakanin su
Tsagin Ƴan Ta’addan Boko Haram na Ahl as Sunnah lid-Da’awah wa’l-Jihad(JAS) ta kashe Mayaƙan ISWAP a wani faɗa daya kaure tsakanin su a Dajin Sambisa.
Daily Trust ta ruwaito cewar tsagin Boko Haram sun farmaki tawagar Tsagin ISWAP da daddare a ranar Lahadi 22 ga watan Mayu, a tsakanin yankin Kaffa zuwa Litawa a Ƙaramar Hukumar Damboa ta Jahar Borno, kamar yadda wani masanin tsaro da ta’addanci Zagazola a yankin Tafkin Chadi ya bada rahoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Talauci ko Neman Sauƙi: Rahoto ya nuna ƙaruwar sayen Tsofaffin wayoyin iPhone, Samsung da Kashi 10 a Najeriya
Wata Majiyar Sirri ta shaidawa Masanin cewa mayaƙa 6 sun rasa rayukansu, a yayinda aka lalata Abun Hawan su.
Majiyoyin sun ce “da misalin ƙarfe 7, Mayaƙan ISWAP a cikin motoci 6, da Mashina 3 sun isa yankin Kaffa domin ɗauke gawarwakin, zuwa Wajiroko.
“Faɗan cikin gidan yana cigaba da ƙaruwa a tsakanin Ƙungiyoyin ta’addancin, inda yanzu sun koma suna farautar juna su da zaran sun samu nasara,” Inji Majiyar
Comments 1