Jam’iyyar (APC) mai mulkin Kasa da jam’iyyar hamayya ta PDP a Borno sun shiga yakin cacar baki kan yadda ake cigaba da tsugunar da ‘yan gudun hijirar da suke gudun hijira.
Ana sake tsugunar da ‘yan gudun hijira a sansanonin da suke Maiduguri zuwa shedikwatar karamar hukumarsu.
Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na Jihar, Amos Adziba ya fitar, ya yi kira da a binciki makudan kudaden da aka kashewa wajen sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar.
Da yake mayar da martani kan matsayar PDP, shugaban jam’iyyar APC a jihar, Ali Dalori ya bayyana kiran PDP a matsayin abun takaici da kuma nuna rashin damuwa da halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki.
PDP ta yi ikirari a cikin sanarwarta cewa gwamnatin jihar karkashin jam’iyyar APC ba za ta iya kashe Naira miliyan 500 ba wajen tsugunar da fursunonin sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi kamar yadda ta yi ikirari.
Ta yi ikirarin cewa gwamnatin APC tana wasa ne kawai da batun ‘yan gudun hijira don samun maki na siyasa mai arha. Al’ummar Borno sun fi kowa sanin gaskiyar lamarin da kasar ke ciki, musamman rashin wutar lantarki, hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi, yayin da ake cigaba da rufe kasuwanni da dama.
Shi ma shugaban jam’iyyar APC, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP da ta kwanta dama a Borno na bukatar ta hada kai da sauran masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa shirin tsugunar da ‘yan gudun hijira a maimakon yin amfani da halin da take ciki wajen taka siyasar yakin neman zabe.
“Yayin da mutane, ba tare da la’akari da jam’iyya ko addini ba, game da kungiyoyin kasa da kasa suna yabawa matakan da gwamnati ta dauka na magance matsalar rashin tsaro, ‘yan uwanmu a jam’iyyar PDP, saboda dalilan da aka fi sani da su sun zabi zama kanana ta hanyar siyasantar da harkokin tsaro.
“Ina so in roke su da su nuna kishin kasa a matsayinmu na ’yan Borno inda muka zabi yin aiki tare don samar da zaman lafiya da cigaba ta hanyar tallafawa tsarin tare da bayar da gudunmawar su don tallafa wa ‘yan gudun hijirar kamar yadda sauran masu ruwa da tsaki a gida da waje suke yi.
“Ban ga wani laifi ba wajen karfafawa marasa galihu, musamman ‘yan gudun hijirar da aka ba wa kowane magidanci Naira 100,000 da kuma Naira 50,000 ga mata tare da kayan abinci,” in ji Mista Dalori.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa gwamnatin Borno a kudurinta na rufe dukkanin manyan sansanonin dake Maiduguri zuwa karshen watan Disamba, ya zuwa yanzu ta sake tsugunar da ‘yan gudun hijira daga manyan sansanoni guda uku.