Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, wanda kuma shine shugaban Gidaniyar Ganduje foundation ne ya jagoranci musuluntar da maguzawa tare da basu tallafin dogaro da kai da kuma kayayyakin sawa a Garin Gidan Goje dake Karamar Hukumar Takai.
A jawabinsa na farko Gwamna Ganduje ya fara da tambayar maguzawan da za su karbi Musuluncin akan me yasa zasu shiga addinin Musulunci? Inda suka ce; Ra’ayin kan su ne suka yanke shawarar shiga addinin ba tare da wani ya tilasta musu ba kuma ba don za’a basu wani abu ba.
Daga nan ne Gwamnan ya laqqanawa wani kaso cikin mutunen 314 kalmar Shahada wacce ta ke tabbatar da kasancewar su musulmai.
Sannan Gwamnan yayi kira a gare su da su kasance masu bin dokokin addinin Musulunci musamman wajen gujewa dukkannin aikata sabo da rike dlgaskiya da gmana a rayuwar su.
Haka zalika yayi alkawarin, Gidauniyar Ganduje zata gina babban masallacin Juma’a da makaranta domin ilimantarwa da kara dabbaka addinin Musulunci a Garin na Goje.
A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Izala na Kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yabawa kokarin wannan Gidauniya bisa yadda take kokarin dabbaka addinin Musulunci bisa Jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sheikh Bala Lau da sauran malamai wanda suka hada da shugaban kungiyar Izala na Kano, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da wakilin Shugaban darikar Kadiriyya Sheikh Kariballah Nasiru Kabara, da Sauran manyan malamai daga kungiyoyi daban-daban da kuma shugaban karamar hukumar Takai (Algon) Hon. Bappa Takai da mallam Salihu Sagir Takai da Sauran manyan mutane suma sun laqanawa wasu cikin maguzawan kalmar Shahada.
A nata bangaren, Wakiliyar Mai dakin Gwamnan kuma mamba a Gidauniyar ta Ganduje foundation Doctor Amina Abdullahi Ganduje ta bayyana farin cikin ta bisa yadda mahaifin nata ya dora su akan hanyar hidimtawa addinin Musulunci da al’umma inda ta tabbatar da cewa zasu cigaba da hidimtawa addinin Musulunci a karkashin wannan Gidauniya musamman wajen gina Makarantu, Masallatai, Asibitoci, Aikin Ido da sauran ayyukan wannan Gidauniya.
Daga karshe, Doctor Amina Ganduje ta bi sahun mahaifin nata wajen laqqanawa wani kaso cikin 314 kalmar Shahada domin tabbatar da su a cikin addinin Musulunci.