An kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama yayin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne na Boko Haram suka kai farmaki kauyen Kilangar da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno a ranar Lahadi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Klangar al’umma ce a majalisar Askira Uba inda mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Engr Abdullahi Askira ya fito.
Majiyoyi sun ce ‘yan ta’addan a ranar Lahadin da ta gabata sun kuma kaiwa Hakimin Kilangar, Alhaji Abdullahi Adamu Kilangar farmaki.
Majiyar ta bayyana cewa, ‘yan ta’addan dauke da makamai sun afkawa al’ummar da misalin karfe 2:00 na rana inda suka fara harbe-harbe a wuraren da suka nufa tare da kona gidaje, motoci, shaguna da kuma kwashe dukiyar jama’a.
“A halin yanzu muna cikin bala’i yayin da ‘yan tada kayar baya suka abka cikin al’ummarmu, suna harbe-harbe a wasu wurare tare da kona gidaje, motoci, shaguna da kuma sace-sace.
“Ko da yake ba zan iya fada muku adadin wadanda suka mutu ba, amma an kashe mutane da dama tare da lalata kadarori ba tare da wata arangama daga jami’an tsaro ba.” Majiyar al’ummar da ta yi sa’a ta tsere ta bayyana.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin kakakin majalisar jihar, Abdullahi Askira, ya ce, “kusan mutane 7 ne suka mutu tare da kona gidan Hakimin, da lalata motoci 7.
“Hakazalika, maharan sun yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba, kuma sun yi awon gaba da motoci biyu, bayan sun yi awon gaba da kayan abinci da dabbobi a cikin al’umma.” Inji mataimakin shugaban majalisar.