Wata budurwa tayi wuff da wani bature wanda har ya baro inda yake rayuwa ya zo garin su.
Bidiyon wanda aka sanya a TikTok ya nuna yadda baturen ya baro ƙasar su domin haɗuwa da ƴan’uwan masoyiyar sa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KARANTA KUMA: Na cika alkawarin da na ɗauka kan Boko Haram -Shugaba Buhari
Wani mai amfani da Cafe Au Lait shine ya sanya bidiyon, inda baturen yake cewa yana jindaɗi da kuma tsoron yadda zata kaya.
Budurwar da baturen saurayinta tare suna taho daga ƙasar shi zuwa nahiyar Afrika.
Masoyan biyu an nuna su a filin jirgi lokacin da suke shirin tashi sannan da kuma lokacin da suka iso ƙauyen su budurwar.
Suna isowa ƙauyen, ƴan’uwan budurwar suka tarbe su hannu bibbiyu.
A wani ɓangare na bidiyon, baturen ya nuna kaɗuwarsa kan yadda a matsayin sa na namiji aka ƙi barin sa da ya taimaka da ƴan aikace-aikacen gida.
Ku kalli bidoyon a nan
Bidiyon ya ɗauki hankulan mutane da dama inda suka yi ta tofa albarkacin bakin su.
Ga kaɗan daga ciki:
@stellahumble ta rubuta:
“Duk lokacin da na ga mutane na cikin farin ciki a soyayya, ina so na jaraba nima amma sai dai bani da sa’a a soyayya. Ba damuwa ina maka barka za zuwa Afrika.
@user7488133714612lavender ya rubuta:
“Wow! Ina taya ku murna! Ina fatan na samu nawa nima nan bada daɗewa ba. Ban sani ba ko ni kaɗai ne mai rashin sa’a. Ina fatan Ubangiji ya shiga lamarin.
Ɗan Najeriya Yayi Wuff Da Kyakkyawar Baturiya, Har Ta Kai Shi Ganin Iyaye
A wani labarin na daban kuma, wani ɗan Najeriya yayi wuff da kyakkyawar baturiya, har ta fara zaga dangi da shi.
Wata budurwa baturiya ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna lokacin da ta kai saurayin ta ɗan Najeriya domin ya gaisa da ƴan’uwanta lokacin shagalin bikin Kirismeti.
Baturiyar wacce ƴar ƙasar Poland ce ta bayyana cewa duk da ta san cewa saurayin nata yayi nesa da gida, tana son tayi duk wani abu mai yiwuwa domin ganin ya samu sakewa yaji kamar a Najeriya yake.