Duk da dai mata suna iyakar ƙoƙarinsu wurin ganin sun saye zuciyar iyayen samarinsu kafin aure, a wannan ɓangaren abu daban ne, Legit.ng ta ruwaito.
Wata budurwa ‘yar Indonesia ta rabu da saurayinta bayan mahaifiyarsa ta sa ta wanke-wanke.
KU KARANTA: Yadda tsohon saurayina ya koma ɗan daudu, yanzu ɗan diras da sikel yake sa wa, Budurwa
A ganinta da alamu mahaifiyar saurayin za ta tasa ta da aiki idan ta aure shi, hakan yasa ta ɗauki matakin.
Belladeasy ta ki yin wanke-wankan a ranar 25 ga watan Nuwamba, kuma ma’abociyar TikTok din ta ce ta zaci matar za ta ce ta bar kayan wanke-wanken a teburin.
Ta ce ta yi mamakin yadda matar ta sa ta aiki duk da ta taya ta girki, bayan ta tambayeta idan ta iya girki.
A cewarta, zuwa gaisar da iyaye ba abu bane wanda zai sa a dinga sa mace aikin wahala ba.
A cewarta ta dauki matakin ne na kin yin wanke-wanken ganin yadda matar ta dage kan cewa lallai sai ta yi aikin.
An sha kunya: Yadda budurwa ta ɓurma salgar gidan iyayen saurayinta daga zuwa gaishe su
Wata budurwa mai suna Kennedy Calwell daga Vancouver, Canada ta ragargaza salgar gidan iyayen saurayinta yayin da ta kai musu ziyara ta farko, LIB ta ruwaito.
Ta ziyarci iyayen Nick ne a karon farko inda wannan mummunan lamarin ya auku da ita. Sai da ta bar garinsu zuwa Toronta inda ta kai musu ziyara, saidai yayin da ta shiga bandaki inda ta kasa yin filoshin din bayan gidan da ta yi.
Yayin da ta dage tana kokarin korawa kawai sai ta balle mazaunin salgar wanda ya farfashe. Calwell ta dauki bidiyon yadda lamarin ya auku a wani bidiyo ta asusunta na TikTok.