Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis ya karbi bakuncin tawagar bankin Bunkasa tattalin arzikin yankin kasashen Larabawa wato Arab Bank for Economic Development (BADEA) a fadarsa na Aso Rock Villa, dake Babban Birnin Tarayya Abuja. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tawagar ta samu rakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda ya koma bakin aiki a ranar Litinin din da ta gabata a daidai lokacin da ake rade-radin cewa ya na fuskantar barazana ga matsayinsa a babban bankin kan batutuwan da ya ke da alaka da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Shugaban PDP da Mataimakin Sa, Wasu Sun Sauya Sheka Zuwa APC
Da Emefiele ya dawo kasar a ranar litinin, labari ya fara yawo cewa DSS sun mamaye bankin, suna neman kama shi, amma hukumar ta musanta hakan.
Kazaliak Babban bankin na CBN ya sanar da cewa gwamnan baya kasar ne bayan ya kasa gurfana a gaban majalisar wakilai da ta kira shi kan wasu manufofin bankin a karshen shekarar da ta gabata.
Wadanda suka halarci taron a ranar Alhamis din nan da shugaban kasa sun hada da shugaban ma’aikatan fadar sa, Farfesa Ibrahim Gambari, ministan harkokin waje, Mista Geoffrey Onyeama, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, babban sakataren ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa. Alhaji Aliyu Ahmed.
Sauran sun hada da tawagar bankin na Larabawa, da suka hada da Babban Darakta na BADEA, Dr Sidi Ould Tah, Jakadan Najeriya a Sudan, H.E Safiu Olamyan, Daraktan Ayyuka na Jama’a, Mista Diab Karrar Ahmed Karrar, Shugaban Sashen Ayyuka na BDS, Yousif Awad Ahmed da Mataimakinsa. Daraktan (GIU), Mista Mustapha Jimoh.
A wani labari kuma, Tsohon Shugaban Majalissar Dattijai, Wayas Ya Mutu Ne Saboda Talauci, Ba Rashin Lafiya Ba, Inji Dan
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Joseph Wayas ya mutu ne saboda talauci ba rashin lafiya ba, kamar yadda dansa na farko, Joseph Wayas Jr, ya ce.
Jr Ya ce mai yiwuwa mahaifinsa yana raye idan ya samu kulawar da ta dace.