Wasu tagwayen fashewa sun afku inda ya yi sanadin raunata mutane uku a wani gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a filin wasa na Rumu-Woji, dake Fatakwal.
An tattaro cewa akalla mutane uku ne suka jikkata a lamarin da ya faru a yammacin ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Shugaban Majalissar Dattijai, Wayas Ya Mutu Ne Saboda Talauci, Ba Rashin Lafiya Ba — Dansa
Majiyar JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa biyu daga cikin wadanda suka jikkata mata ne kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Darlington Nwauju, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin “abin takaici ne”.
A wani labarin kuma, 2023: Shugaban PDP da Mataimakin Sa, Wasu Sun Sauya Sheka Zuwa APC
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Dabaza a karamar hukumar Kazaure a jihar Jigawa, Abubakar Sani tare da wasu shugabannin jam’iyyar sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Shugaban karamar hukumar Kazaure Muhammad Mukhtar Zanna ne ya bayyana haka a lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka a Jigawa.