Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasa da ta soke wani sashe na dokar zabe wanda ya haramtawa masu rike da mukaman siyasa shiga takara.
Buhari ya bukaci hakan ne yayin da yake sanya hannu a kan kudirin dokar a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Juma’a.
Sa’o’i kadan kafin ya sanya hannu kan kudirin, Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda Buhari da makusantansa ke cikin rudani kan makomar wadanda suka nada shi a siyasance wadanda za su iya yin murabus da yawa idan kudirin ya zama doka.
Sashi na 84 (12) na kudirin ya sanya wajabcin yin murabus daga mukaman siyasa masu son tsayawa takara a 2023.
Wadanda aka nada a wannan fanni ba sa son yin murabus saboda babu tabbacin za su dawo da mukamansu idan sun fadi zaben fidda gwani.
Yayin da yake rattaba hannu kan kudurin dokar, Buhari ya ce sashe na 84(12) na dokar ya sabawa ‘yancin masu rike da mukaman siyasa na kada kuri’a, ko a zabe su a taron jam’iyyun siyasa da na majalisu.